ABNA24 : Shugaba Rauhani ya bayyana hakan ne a yau a okacin da yake ganawa da jami’an hukumomi na kiwon lafiya, inda ya bayyana cewa hakika jami’ai a bangarorin kiwon lafiya sun bayar da gagarumar gudunmawa wajen yaki da cutar corona a kasar.
Ya ci gaba da cewa, a halin yanzu bisa ga dukkanin bayanai da yake samu daga hukumomin kiwon lafiya na kasa da kuma sauran bangarori na kiwon lafiya masu zaman kansu, an samu raguwar kamuwa da cutar cutar corona a fadin kasar.
Haka nan kuma ya yi jinjina ga ma’aikatan kiwon lafiya da suka sadaukar da rayukansu da lokutansu domin ceton al’umma, kamar yadda kuma ya godewa sauran jama’ar kasar kan irin hadin kan da suke baiwa jami’an kiwon lafiya wajen gudanar da ayyukansu.
342/